John 21

Yesu da Kamun Kifin Ban Mamaki

1Daga baya Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiransa, a bakin Tekun Tibariya.
Wato, Tekun Galili
Ga yadda ya faru:
2Siman Bitrus, Toma (wanda ake kira Didaimus), Natanayel daga Kana ta Galili, ʼyaʼyan Zebedi maza, da kuma waɗansu almajirai guda biyu suna tare. 3Sai Siman Bitrus ya ce musu, “Za ni kamun kifi,” suka ce, “Za mu tafi tare da kai.” Saboda haka suka fita suka shiga jirgin ruwa, amma a daren nan ba su kama kome ba.

4Da sassafe, sai ga Yesu tsaye a gaci, amma almajiran ba su gane cewa Yesu ne ba.

5Sai ya ce musu, “Abokai, kuna da kifi kuwa?”

Suka amsa suka ce, “Aʼa.”

6Ya ce musu, “Ku jefa tarunku dama da jirgin ruwan, za ku samu.” Da suka yi haka, sai suka kāsa jawo tarun saboda yawan kifi.

7Sai almajirin da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, “Ai, Ubangiji ne!” Nan da nan da Siman Bitrus ya ji ya ce, “Ai, Ubangiji ne,” sai ya yafa mayafinsa, (don dā ma ya tuɓe shi), ya fāɗa cikin ruwan. 8Sauran almajiran kuwa suka bi shi cikin jirgin ruwan, janye da tarun cike da kifi, don ba su da nisa daga gaci, wajen yadi ɗari ne. 9Da suka sauka, sai suka ga garwashin wuta a can da kifi a kai, da kuma ʼyan burodi.

10Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifin da kuka kama yanzu.”

11Sai Siman Bitrus ya hau ya jawo tarun gaci. Ya cika da manyan kifi, 153, amma duk da yawansun nan tarun bai tsintsinke ba. 12Yesu ya ce musu, “Ku zo ku karya kumallo.” Ba wani daga cikin almajiran da ya yi karambanin tambayarsa, “Wane ne kai?” Sun san cewa Ubangiji ne. 13Yesu ya zo, ya ɗauki burodin ya ba su, haka kuma kifin. 14Wannan fa shi ne sau na uku da Yesu ya bayyana kansa ga almajiransa bayan an tashe shi daga matattu.

Yesu Ya Sāke Tabbatar da Bitrus

15Da suka gama ci, sai Yesu ya ce wa Siman Bitrus, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske fiye da waɗannan?”

Ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.”

Yesu ya ce, “Ciyar da ʼyaʼyan tumakina.”

16Har wa yau Yesu ya ce, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske?”

Ya amsa ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.”

Yesu ya ce, “Lura da tumakina.”

17Sau na uku ya ce masa, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata?”

Sai Bitrus ya ɓata rai saboda Yesu ya tambaye shi sau na uku, “Kana ƙaunata?” Ya ce, “Ubangiji ka san kome duka; ka san cewa, ina ƙaunarka.”

Yesu ya ce, “Ciyar da tumakina.
18Gaskiya nake faɗa maka, saʼad da kake saurayi kakan yi wa kanka sutura ka tafi inda ka so; amma saʼad da ka tsufa za ka miƙa hannuwanka, wani dabam yǎ yi maka sutura yǎ kai ka inda ba ka so.” 19Yesu ya faɗi wannan ne, don yǎ nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi yǎ ɗaukaka Allah. Saʼan nan ya ce masa, “Bi ni!”

20Bitrus ya juya ya ga cewa almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana binsu. (Wannan ne ya jingina a jikin Yesu saʼad da suke cin abincin yamman nan da ya ce, “Ubangiji wane ne zai bashe ka?”) 21Da Bitrus ya gan shi sai ya ce, “Ubangiji, wannan fa?”

22Yesu ya amsa, ya ce, “In na so yǎ kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki? Kai dai bi ni.” 23Saboda wannan, jita-jita ta bazu a cikin ʼyanʼuwa cewa wannan almajirin ba zai mutu ba. Amma fa Yesu bai ce ba zai mutu ba; shi dai ya ce, “In na so yǎ kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki?”

24Wannan shi ne almajirin da ya ba da shaida a kan waɗannan abubuwa ya kuma rubuta su. Mun san cewa shaidarsa gaskiya ce.

25Yesu ya yi waɗansu abubuwa da yawa kuma. Da a ce an rubuta kowannensu, na tabbata ko duniya duka ba za ta sami wuri saboda littattafan da za a rubuta ba.

Copyright information for HauSRK